Lyon na son ta kara da Marseille a filin da bana kowa ba

Lyon za ta daukaka kara kan hukuncin da aka yanke na zuwa gidan Marseille, saboda tana son buga tamaula ba tare da fargaba ba.

Ranar 28 ga watan Oktoba magoya bayan Marseille suka kai wa motar ‘yan wasan Lyon hari a Stade Velodrome dalilin hakan ta kai an dakatar da wasan.

Masu shirya gasar Ligue 1 sun sanar cewar za a buga fafatawar ranar 6 ga watan Disamba, kuma an amince ‘yan kallo za su iya shiga sitadiya a ranar.

Leave a comment