An bayyana Noah Lyles a matakin gwarzon dan wasan motsa jiki na duniya na 2023.
Dan kasar Amurka ya lashe lambar yabo ta zinare uku a gasar duniya a tsere.
Haka shima dan kasar Sweden, Armand ‘Mondo’ Duplantis ya lashe kyauta, bayan da ya yi fice a tsallen kwangwala a fili da a rufaffen dakin wasa.
‘Yar kasar Kenya, Faith Kipyegon ce ta lashe kyautar mata, wadda ta kafa tarihin bajinta uku a gudun dogo da gajeren zango a 2023.
‘Yar kasar Venezuela, Yulimar Rojas tana cikin wadanda suka karbi kyauta, wadda ta lashe lambar bajinta ta hudu a tsallen yashi.
Jerin wadanda aka karrama:
- Women’s track: Faith Kipyegon (KEN)
- Women’s field: Yulimar Rojas (VEN)
- Women’s out of stadia: Tigist Assefa (ETH)
- Men’s track: Noah Lyles (USA)
- Men’s field: Armand “Mondo” Duplantis (SWE)
- Men’s out of stadia: Kelvin Kiptum (KEN)