Luton za ta karbi bakuncin Arsenal a Premier

Arsenal za ta je gidan Luton Town, domin buga wasan mako na 15 a gasar Premier League ranar Talata.

Arsenal tana matakin farko a kan teburi da tazarar maki biyu tsakaninta da Liverpool ta biyu da maki uku tsakaninta da Manchester City.

Wannan shi ne wasan farko da za su kara a tsakaninsu, tun bayan da Luton ta ci Arsenal 1-0 a 1991.

Gunners ba ta samu nasara ba a wasa 10 a gidan Luton, tun bayan da ta ci 2-1 a Janairun 1984.

Luton Town tana cikin kungiyoyi uku da kwallaye ke shiga ragarsu, sauran sune Brighton da Sheffield United.

Arsenal ta yi nasara a wasa uku a lik a waje da cin 1-0 a kakar nan.

Haka kuma Gunners ta lashe wasa bakwai a Premier League a Disamba.

Leave a comment