London zai karbi bakuncin bikin Fifa Best 2023

Birnin London zai karbi bakuncin bikin karrama gwarzayen kwallon kafa na duniya na 2023 ranar 15 ga watan Janairun 2024.

A bikin ne za a karrama fitatce da fitatciyar ‘yar wasan tamaula a duniya da kwallon da aka ci mafi kayatarwa da tawaga mafi kwazo da suka fi kwazo a 2023 da sauransu.

Fifa bai fayyace wurin da za a gudanar da bikin ba, amma wasu kamfanin dillacin labarai na cewar a cikin watan nan mahukunta za su je su zabi wurin da zai fi dacewa.

Wannan shi ne karo na uku kenan da birnin London zai gabatar da bikin, bayan wanda ya yi a 2016 da kuma 2017.

Cikin wadanda ke takara a maza har da dan wasan tawagar England da Arsenal, Declan Rice da na Manchester City, Julian Alvarez da Kevin De Bruyne da Erling Haaland da Bernardo Silva da tsohon dan wasan City, Ilkay Gündogan.

Kociyan Man City, Pep Guardiola yana cikin masu horar da tamaula da ke takarar kociyan da ba kamarsa a 2023.

Ciki har da na Tottenham, Ange Postecoglou. Cikin masu takarar tsare raga sun hada da na Manchester City, Ederson da na Manchester United, Andre Onana, wanda ya taimaki Inter Milan ta kai wasan karshe a Champions League a 2023.

Ana auna kwazon wadanda suka yi bajinta a kwallon kafa a duniya daga 19 ga watan Disamba zuwa 20 ga watan Agustan bana.

A fannin mata kuwa, masu takara sun hada da ‘yan wasa biyar daga England.

Yayin da Mary Earps tana takarar mai tsaron ragar da ba kamarta, haka kuma Rachel Daly da Alex Greenwood da Lauren James da kuma Keira Walshduk suna cikin takara.

Masu takarar koci kuwa sun hada da Sarina Wiegman da wadda ta horar da Chelsea, Emma Hayes.

Ana auna kwazon mata ne daga 1 ga watan Agustan 2022 zuwa 20 ga watan Agustan 2023, zuwa karshen wasan gasar kofin duniya da aka yi a Australia da New Zealand.

Lionel Messi, wanda ke cikin takara, shine ya lashe kyautar 2022, bayan da ya taimakawa Argentina ta ci kofin duniya a Qatar a 2022 a Qatar.

A bangaren mata kuwa ‘yar wasan Spain da Barcelona, Alexia Putellas ce ta lashe kyautar.

Leave a comment