Ranar da Arsenal ta doke Tottenham 3-2 a gasar Premier League ranar Lahadi shi ne wasa na bakwai da ta yi nasara a karawar hamayya ta ‘yan birnin Landan a bana.
Kungiyoyi bakwai ne dake birinin Landan dake buga Premier League da ake karawa 12 a kaka daya, wanda Arsenal ta yi ranar Lahadi shi ne na karshe a kakar nan.
Cikin wasannin ta hada maki 24 daga wasa 12, kenan ita ce ta daya a karawa tsakanin kungiyoyin Landan a Premier League a kakar nan.
Chelsea ce ta biyu da maki 17, wadda ta buga wasa 10, sai Fulham mai maki 15 mai wasa 11 da maki 15.
Jadawalin wasannin hamayyar birnin Landan a 2023/24
Kungiya P W D L F A Pts
Arsenal 12 7 3 2 30 13 24
Chelsea 10 5 2 3 17 17 17
Fulham 11 4 3 4 15 12 15
Tottenham 11 4 3 4 19 21 15
West Ham 11 4 2 5 17 27 14
Brentford 11 3 3 5 19 20 12
Crystal Palace 12 2 4 6 15 22 10
Karawar farko da ta fara yi ta hamayya a bana ita ce wadda ta je ta yi rashin nasara a Fulham 2-1, sai suka tashi 2-2 a wasa na biyu a Emirates.
Kenan Fulham ce kadai Arsenal ba ta ci ba a Craven Cottage a cikin watan Disamba.
Wasan da Arsenal ta tashi 2-2 da Fulham a gida, shi ne canjaras na uku da ta yi a bana a karawar hamayya, bayan da ta yi da Tottenham da wanda ta yi a Chelsea a Stamford Bridge.
A watan Nuwamba Arsenal ta ci Brentford 1-0 daga nan ta lallasa Crystal Palace 5-0 da doke West Ham United 6-0 a watan Fabrairu.
Sai wasa na biyu da Gunners ta ci Brentford, sannan ta zura 5-0 a ragar Chelsea a cikin watan Afirilu.
Arsenal, wadda take ta daya a kan teburi za ta karbi bakuncin Bournemouth a wasan mako na 36 a Emirates.