Bayanai kan wasan Liverpool da Arsenal a Premier League

Liverpool za ta karbi bakuncin Arsenal a wasan mako na 19 ranar Asabar a gasar Premier League a Anfield.

Arsenal ce ta daya a kan teburi mai maki 39, iri daya da na Aston Villa ta biyu da tazarar maki daya tsakanin Liverpool da Gunners.

A kakar bara a Premier League Arsenal ta ci Liverpool 3-2 a Emirates ranar 9 ga watan Oktoban 2022.

A wasa na biyu a Anfield sun tashi 2-2 ranar 9 ga watan Afirilun 2023.

Watakila dan wasan Liverpool, Ryan Gravenberch, wanda a baya aka ce ya ji rauni ya buga wasan.

Sai a cikin sabuwar shekara ake sa ran Alexis Mac Allister da Diogo Jota da Andrew Roberton za su murmure.

Dan wasan Arsenal, Mohamed Elneny na daf da komawa buga tamaula, amma da kyar ne idan Jorginho zai yi karawar.

Har yanzu Thomas Partey da Jurrien Timber da Takehiro Tomiyasu da Fabio Vieira na jinya.

Wasan hamayya tsakanin Liverpool da Arsenal

Cikin wasa 10 baya Liverpool ba ta yi rashin nasara ba a gida a Premier a hannun Arsenal, inda ta ci bakwai da canjaras uku.

A fafatawa 15 baya Liverpool kan zura kwallo a ragar Arsenal, wadda ta ci 43 a cikin karawar.

Wannan shi ne karo na 100 da Liverpool za ta karbi bakuncin Arsenal a gida a lik.

Batun da ya shafi kwazon Liverpool

Wasa daya aka doke Liverpool daga 50 da ta buga a Anfield, wadda ba a doke ta 20 baya a jere.

Wasan da Liverpool ta tashi da Manchester United 0-0 shi ne karon farko da ba ta zura kwallo a raga ba a fafatawa 26 a jere.

Wasa uku Liverpool ta yi rashin nasara daga 41 da ta buga a gida da kungiyoyin da ke ‘yan shidan farko, wadda ta ci 22 da canjaras 16.

Mohamed Salah ya ci Arsenal kwallo tara daga wasa 13 har da dayan da ya ci a lokacin da yake Chelsea.

Trent Alexander-Arnold ya bayar da kwallo shida aka ci Arsenal a Liverpool, biyar daga ciki a Anfield.

Batun da ya shafi kwazon Arsenal

Arsenal ta yi nasara a wasa bakwai daga tara baya da ta buga a dukkan fafatawa da canjaras daya da rashin nasara daya.

Shi ne wanda Aston Villa ta doke ta 1-0 – watakila ta yi rashin nasara biyu a jere a wasan waje a karon farko tun Mayun 2022.

Gunners ta lashe wasa 24 daga 39 a Premier League a 2023, mai canjaras takwas da rashin nasara bakwai.

Gabriel Martinelli ya ci Liverpool kwallo hudu a bara ya zura daya a raga ya kuma bayar an ci Liverpool.

Gabriel Jesus ko dai ya zura kwallo a raga ko kuma ya bayar a ci a wasa uku da ya je Anfield, wanda shi ne ya ci na biyun da suka 2-2 a bara.

Leave a comment