Liverpool ta koma ta daya a kan teburin Premier League

Liverpool ta doke Sheffield United 3-1 a wasan mako na 31 da suka fafata a Premier League a Anfield ranar Alhamis.

Liverpool ta ci kwallayen ta hannun Darwin Nunez da Alexis Mac Allister da wadda Cody Gakpo ya ci daf da za a tashi daga karawar, yayin da Conor Bradley ya ci gida.

Liverpool ta ci kwallo 26 a Premier League a lokacin da ake daf a tashi daga wasa, wasu lokutan tun daga saura minti 15 a busa tashi kungiyar Abfield kan zura kwallo ko kwallaye a raga.

Kwallon da Darwin Núñez ya ci kenan yana da hannu a ci wa Liverpool 15 a bana a dukkan karawa a 2024, wanda ya ci kwallo 10 ya kuma bayar da biyar aka zura a raga – shi ne kan gaba a wannan bajintar.

Da wannan sakamakon Liverpool ta koma ta daya a kan teburin Premier League da maki 70 da tazarar biyu tsakani da Arsenal ta biyu, yayin da Manchester City ce ta uku mai rike da kofin bara mai maki 67.

Liverpool za ta je Old Trafford ranar Lahadi 7 ga watan Afirilu domin buga wasan mako na 32 da Manchester United a Premier League.

Leave a comment