Liverpool ta kai zagaye na biyu a Europa League

Liverpool ta kai zagaye na biyu a Euopa League, bayan da ta caskara LASK 4-0 a Aanfield ranar Alhamis.

Wadanda suka ci mata kwallayen sun hada da Luis Diaz da Mohamed Salah da kuma Cody Gakpo.

Itama Bayern Leverkusen ta kai zagayen ‘yan 16 da za su ci gaba da Europa League, bayan nasara a kan Hecken da ci 2-0.

Ita kuwa Freiburg tana cikin ‘yan biyun farko a teburi, wadda ta caskara Olympiacos 5-0.

A kakar bara Leverkusen ta kai daf da karshe a Europa, wadda Roma ta fitar da ita daga wasannin.

Ajax ba za ta kai zagayen gaba ba, bayan da Olympique Marseille ta yi nasara a kanta da ci 4-3.

Kungiyar Netherlands za ta fuskanci AEK Athens, domin neman gurbin komawa buga Conference League.

Wannan sakamakon ne ya kara bai wa Freiburg damar zama cikin yan biyun farko a teburi.

Kungiyar Jamus tana mataki na biuu a rukunin farko da maki 12 iri daya da na West Ham, wadda ke jan ragama, wadda ta doke Backa Topola 1-0.

Freiburg da West Ham za su kara a wasan karshe na cikin rukuni, duk wadda ta samu nasara za ta kai zagayen gaba kai tsaye.

Wadda ta yi ta biyu kuwa za ta je ta buga wasannin cike gurbi.

A wasannin cike gurbi za a hada kungiya da wadda ta yi ta uku a Champions League, domin neman gurbin ci gaba da wasa a Europa League.

Leave a comment