Liverpool ta barar da damar hawa kan teburin Premier League

Manchester United da Liverpool sun tashi 2-2 a wasan mako na 32 a Premier League da suka kara ranar Lahadi a Old Trafford.

United ta ci kwallayen ta hannun Bruno Fernandes da Kobbie Mainoo, yayin da Luis Diaz da Mohamed Salah suka ci wa Liverpool kwallayen.

Da wannan sakamakon Liverpool tana mataki na biyu da maki 71 iri daya da na Aarsenal, amma da tazarar rarar kwallaye tara a tsakaninsu.

Wannan shi ne wasa na uku da suka fuskanci juna a tsakaninsu a bana, inda suka fara tashi ba ci a Premier a Anfield, sannan United ta fitar da Liverpool a FA Cup da cin 4-3 a Old Trafford.

Yauzu dai Liverpool na bukatar ko dai Arsenal ta barar da maki, ko kuma kungiyar Anfield ta zura kwallaye a raga fiye da na Arsenal, koda za su kare kakar bana da maki iri daya.

Manchester City ce ta uku da tazarar maki daya tsakaninta da Liverpool da kuma Arsenal, bayan da kowacce ta yi karawa 31 a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Dukkansu suna da wasa mai sarkakiya a gabansu da za su fuskanci Tottenham, Arsenal za ta kara da Manchester United, yayin da Liverpool da Arsenal za su fuskanci Aston Villa.

Wasannin mako na 33 a Premier League

Saturday 13 April 2024

  •               Newcastle United da Tottenham
  •               Manchester City da Luton Town 
  •               Burnley da Brighton
  •               Nottingham Forest da Wolverhampton
  •               Brentford da Sheffield United  
  •               Bournemouth da Manchester United  

Lahadi 14 ga watan Afirilu 2024

  •               Liverpool da Crystal Palace 
  •               West Ham United da Fulham  
  •               Arsenal da Aston Villa 

Litinin 15 ga watan Afirilu 2024

  •               Chelsea da Everton

Leave a comment