Liverpool ta amince ta dauki Slot madadin Kloop

Arne Slot ne zai zama kociyan Liverpool, domin maye gurbin Jurgen Kloop, bayan da ta cimma yarjejeniya da Feyenoord.

Mai shekara 45 zai karbi daga dan kasar Germany, wanda cikin watan Janairu ya sanar zai ajiye aikin jan ragamar kungiyar Anfield, bayan sheakara tara.

Slot ya ja ragamar Feyenoord ta lashe Eredivisie a 2022/23, wanda ya dauki Dutch Cup a bana, inda kungiyar take ta biyu a teburin kakar nan.

An ce dalilin da Liverpool za ta dauke shi, ya zama kociyanta da yadda yake koyar da salon kai hare-hare da yadda ya kware wajen bunkasa matasa ‘yan wasa.

Slot ya karbi aikin horar da Feyenoord a 2021, kuma tun bayan da ya fara abin kirki aka yi ta alakanta shi da zai koma horar da tamaula a kungiyar Premier League har da Tottenham da ta so ya zama mai horar da ita a 2023.

Tun farko Liverpool ta yi tayin bai wa Xabi Alonso aikin kociyanta, amma ya zabi ci gaba da horar da Bayern Leverkusen, wadda ta dauki Bundesliga na bana na farko a tarihi.

Haka kuma kungiyar ta kai wasan karshe a German Cup, sannan ta kai zagayen daf da karshe a Europa League.

Alonso mai shekara 42 ya sanar da Liverpool a cikin watan maris cewar, zai ci gaba da horar da Bayern Leverkusen domin ya kara samun gogewa.

An alakanta kocin, Sporting Lisborn, Ruben Amorin da cewar tun farko shi ne zai maye gurbin Klopp a Anfield, wanda ya fara aiki tun daga Oktoban 2015.

Leave a comment