Liverpool da Chelsea za su yi kokarin sayen Vinicius kan £171m

An bayar da rahoton cewar Liverpool da Chelsea na shirin sanar da Real Madrid cewar za su taya Vinicius Junior, domin ya koma buga Premier League kan £171m.

Mai shekara 23 ya koma Santiago Bernabeu da taka leda daga Flamengo a 2018, wanda kawo yanzu ya buga karawa 253 a dukkan fafatawa da cin kwallo 77, sannan ya bayar da 72 aka zura a raga.

Vinicius ya lashe kofin La Liga biyu da Copa del Rey da kuma Champions League, wanda ke fatan jan ragamar kungiyar ta ci gaba da taka rawar gani a Spain da kuma gasar Turai.

Dan kasar Brazil ya ci kwallo 18 ya bayar da takwas aka zura a raga a bana a kungiyar da Carlo Ancelotti ke jan ragama, wanda ya kulla yarjejeniyar ci gaba da taka leda a Real cikin Oktoba, wadda za ta karkare a karshen kakar 2027.

To sai dai an dade ana ta rade-radi kan makomar Vinicius a Real Madrid tun bayan da aka Kylian Mbappe ya sanar cewar zai koma Santiago Bernabeu a karshen kakar nan daga Paris St Germain.

Haka kuma dan kasar Brazil na fama da kalubalen cin zarafi da kalaman wariya da ake yi masa a wasu filayen tamaula a Soain.

Leave a comment