Liverpool da Aston Villa sun raba maki a Premier

Aston Villa da Liverpool sun tashi 3-3 a wasan mako na 37 a Premier League da suka kara ranar Litinin a Villa Park.

Wadanda suka ci wa Liverpool kwallayen sun hada da mai tsaron ragar Aston Villa, Emiliano Martinez da ya ci, sai Cody Gakpo ya kara na biyu, sannan Jarell Quansah ya zura na uku a raga.

Ita kuwa Aston Villa ta ci kwallayen ta hannun Youri Tielemans da kuma Jhon Duran ya zura biyu da ya bai wa kungiyar damar raba maki da Liverpool.

Da wannan sakamakon Liverpool tana mataki na ukun teburin Premier League da maki 79, yayin da Villa take ta hudu da maki 68, kuma kowacce ya rage mata wasa daya a gabanta.

Liverpool ta buga Europa League a bana, wadda Atalanta ta doke ta a zagayen daf da na kusa da karshe, kuma kungiyar Anfield ta dauki League Cup a kakar nan.

Ita kuwa Aston Villa ta kai daf da karshe a Conference League karon farko da ta taka irin wannan matakin tun bayan shekara 42, amma Olypiacos ta yi waje da ita a gasar bana.

Za a buga wasan mako na 38 na karshe a Premier League ranar Lahadi 19 ga watan Mayu, inda Aston Villa za ta je Crystal Palace a Selhurst Park, ita kuwa Liverpool za ta karbi bakuncin Wolverhampton.

Leave a comment