Lewandowski zai je gasar Euro 2024

Tawagar Poland ta hana Wales kai wa gasar cin kofin nahiyar Turai karo na uku a jere, bayan da suka buga wasan neman gurbin shiga Euro 2024.

Tawagogin sun tashi 0-0 a fafatawar da suka yi a Cardiff ranar Laraba daga nan ta kai ga bugun fenariti, bayan karin lokaci inda Poland ta ci 5-4.

Dan wasan Leeds United, Dan James shi ne ya barar da na shi bugun da ta kai Poland ta samu matakin shiga Euro 2024 da za a yi a Jamus daga 14 ga watan Yuni zuwa 14 ga watan Yulin 2024.

Poland mai Robert Lewandowski za ta buga wasanninta a rukuni na hudu da ya kunshi Netherlands da France da kuma Austria.

Poland’s za ta fara da fuskantar Netherlands ranar 16 ga watan Yuni a Hamburg, sannan ta kece raini da Austria a Berling da kuma France a Dortmund.

Wannan shi ne karo na hudu da Robert Lewandowski zai buga gasar cin kofin nahiyar Turai, wanda ya fara halarta a 2012, wanda ya fara cin kwallo a gasar.

Daga nan ya samu damar buga Euro 2016 da ta 2020, wanda kuma ya buga gasar cin kofin duniya a 2018 a Rasha da wadda aka yi a Qatar a 2022.

Leave a comment