Lewandowski zai ci gaba da wasa zuwa shekara hudu

Robert Lewandowski ya ce yana jin zai ci gaba da taka leda zuwa shekara hudu nan gaba.

Dan kwallon Barcelona, mai shekara 35 na fatan ci gaba da murza leda har zuwa lokacin da zai cika shekara 40 da haihuwa kenan.

‘’Har yanzu ina jin karfi a jiki na, sannan kullum ina da son buga tamaula.’’

‘’Ina jin zan iya ci gaba da wasa zuwa kaka uku ko hudu nan gba, saboda ina jin karfin jiki na.’’

Dan wasan ya sanar da hakan a wata jarida Marca ta Spain a hirar da suka yi shi.

Tsohon dan wasan Bayern Munich ya kara da cewar baya kallonsa a matakin wanda zai yi aikin koci nan gaba.

Bayan da ya zama kan gaba a cin kwallaye a LaLiga a bara a Barcelona, dan wasan na fama da jiya a bana.

Hakan ya sa kwallo bakwai ya zura a raga a wasa 13 da ya buga a LaLiga a kakar nan, amma ya ce hakan bai dame shi ba.

‘’Ina ji a jiki na cewar ina wurin da ya dace a kuma lokacin da ya kamata.’’

Leave a comment