Leverkusen za ta lashe Bundesliga ranar Lahadi a karon farko

Watakila Bayern Leverkusen ta lashe Bundesliga ranar Lahadi, idan ta yi nasara a kan Werder Bremen a wasan mako na 29.

Ranar 25 ga watan Nuwambar 2023, Leverkusen ta je ta ci Werder Bremen 3-0, inda Olivier Deman ya ci daga, sannan Jeremie Frimpong ya kara na biyu Alejandro Grimaldo ya zura na uku a raga.

Bayern Leverkusen tana ta daya a kan teburin Bundesliga da tazarar maki 13 tsakaninta da Bayern Munich ta biyu mai rike da kofin bara.

Bayern Munich ta rage makin dake tsakaninta da Leverkusen daga 16 zuwa 13 ranar Asabar, bayan da ta ci FC Cologne 2-0 a karawar mako na 29, inda Raphael Guerreiro da kuma Thomas Muller suka ci mata kwallayen.

Kenan da zarar Leverkusen wadda har yanzu ba a doke ta ba a bana a dukkan fafatawa za ta lashe Bundesliga na bana da zarar ta ci Werder Bremen ranar Lahadi.

Bayern Munich ta dauki Bundesliga 11 a jere tun daga 2011/12 da Borussia Dortmunda ta lashe kofin.

Bayern have won 11 successive top-flight titles since Borussia Dortmund’s triumph in 2011-12.

Leverkusen wadda ta fuskanci faduwa daga Bundesliga a bara lokacin da Xabi Alonso ya karbi aiki a Oktoban 2022, yanzu tana sa ran lashe kofi uku a kakar nan.

Ita ce ta daya a Bundesliga da take fatan lashe kofin ranar Lahadi, sannan za ta buga karawar karsge a German Cup da Kaiserslauten, sannan ta ci West Ham 2-0 a wasan farko a quarter finals a Europa League ranar Alhamis.

Leverkusen za ta kafa tarihin wasa 29 a jere ba a doke ta ba a Bundesliga ranar Lahadi da zarar ta yi nasaraa kan Werder Bremen ko tashi canjaras.

Leave a comment