Leverkusen ta yi wasa 50 a jere ba a doke ta ba

Bayern Leverkusen ta doke Bochum, wadda ta kare da ‘yan wasa 10 ranar Lahadi a Bundesliga ta kuma yi wasa 50 a jere a dukkan fafatawa ba tare da rashin nasara ba.

Leverkusen ta fara cin kwallo ta hannun Patrik Schick daga baya ta kara na biyu ta hannun Victor Boniface a bugun fenariti.

Amine Adli ne ya kara na uku bayan hutu daga baya Josip Stanisic da Alex Grimaldo suka zura a raga.

Kungiyar da Xabi Alonso ke jan ragama na fatan lashe wasan karshe, ya zama ta buga Bundesliga gabaki daya ba tare da rashin nasara ba.

A karshen mako da za mu shiga Leverkusen za ta buga wasan karshe a Bundesliga a gida da Augsburg ranar Asabar, da zarar ba a doke ta ba a wasan ta zama ta farko da ta buga kakar gabaki daya ba tare da rashin nasara ba.

Wasa daya aka doke Bayern Munich a kakar da ta lashe Bundesliga a 1986-87 da kuma 2012-13.

Haka kuma wadda ta lashe Bundesliga a bana za ta fuskanci Atalanta a wasan karshe a Europa League a Dublin ranar 22 ga watan Mayu, sannan za ta kara a wasan karshe a German Cup da Kaiserslautern a Berlin kwana uku tsakina.

Rabonda Leverkusen ta yi rashin nasara tun cikin Mayun 2023 kenan shekara daya kenan.

Kuma Bochum ce ta yi nasara a kanta 3-0 a filin wasa na Vonovia Ruhrstadion a wasan karshe a Bundesliga a 2022-23.

Leave a comment