Leverkusen ta yi wasa 49 a jere ba tare da an doke ta ba

Bayern Leverkusen ta yi wasa 49 a jere ba a doke ta ba, kuma ta kai wasan karshe a Europa League, bayan da ta tashi 2-2 a gidan Roma ranar Alhamis.

Josip Stanisic ne ya farkewa kungiyar Jamus kwallon a minti na 97, hakan ya bai wa Xabi Alonso damar tashi wasan 2-2, kenan ta kai zagayen karshe da cin 4-2, bayan da Leverkusen ta yi nasara 2-0 a wasan farko a Roma.

Da wannann sakamakon Leverkusen ta yi wasa 49 a jere a dukkan fafatawa ba tare da an doke ta ba da yin nasara 40 daga ciki da canjaras takwas.

Kenan kungiyar da Alonso ke jan ragama ta doke tarihin da Benfica ta kafa a tsakanin Disambar 1963 zuwa Fabrairun 1965.

Tarihin da kungiyar Portugal ta kafa shi ne na farko a matakin wasa da yawa a gasar Turai ba tare da rashin nasara ba, mai wasa 48 kamar yadda Uefa ta sanar, yanzu kuma Leverkusen ta kafa wani.

Leverkusen na fatan lashe kofi uku a bana, bayan da ta fara daukar Bundesliga na farko a tarihi, za ta buga wasan karshe a German Cup, za kuma ta fuskanci Atalanta a Europa League a Dublin ranar 22 ga watan Mayu.

Leave a comment