Leverkusen ta yi wasa na 42 ba tare da an doke ta ba a bana

Bayern Leverkusen ta ci West Ham United 2-0 a wasan farko zagayen daf da na kusa da na karshe a Europa League ranar Alhamis.

Sai da rage sauran minti bakwai a tashi Leverkusen ta zura kwallo a raga ta hannun Jonas Hofmann sai kuma Victor Boniface ya kara na biyu daf a busa tashi daga fafatawar.

Wasa na 42 da kungiyar Germany ta buga a dukkan karawa a bana ba tare da na doke ta ba, wadda ta ci wasa 37 da canjaras biyar.

Kungiyar da Xabi Alonso ke jan ragamar na fatan lashe Bundesliga a bana, bayan da take jan ragamar teburin bana da tazarar maki 16 tsakaninta da Bayern Munich ta biyu.

Haka kuma kungiyar Germany ta kai wasan karshe a bana a German Cup, inda za ta kece raini da Kaiserslautern ranar 25 ga watan Mayu, bayan an kammala Bundesliga kenan.

Ranar Alhamis 18 ga watan Afirilu Bayern Leverkusen za ta je gidan West Ham United, domin buga wasa na biyu don kai wa zagayen daf da karshe a Europa League.

Haka kuma duk wadda ta yi nasara za ta kusakanci AC Milan ko kuma Roma a zagayen gaba, bayan da Roma ta je San Siro ta ci 1-0 ranar Alhamis.

Sauran wasannin da ke gaban Leverkusen

Europa League Alhamis 18 ga watan Afirilu

  • West Ham da B Leverkusen

Bundesliga  Asabar 27 ga watan Afirilu 

  • B Leverkusen da Stuttgart            

Bundesliga  Lahadi 5 ga watan Mayu

  • E Frankfurt da B Leverkusen    

Bundesliga  Lahadi 12 ga watan Mayu

  • Bochum da B Leverkusen    

Bundesliga Asabar 18 ga watan Mayu

  • B Leverkusen da Augsburg           

German Cup  Asabar 25 ga watan Mayu

  • Kaiserslautern da B Leverkusen

Leave a comment