Leverkusen ta kammala zagayen farko ba a doke ta ba a Bundesliga

Bayern Leverkusen ta doke Bochum 4-0 a wasan mako na 16 a gasar Bundesliga, inda Patrik Schick ya ci uku rigis.

Kenan Leverkusen ta kammala zagayen farko ba tare da an doke ta ba da tazarar maki hudu tsakaninta da Bayern Munich ta biyun teburi.

Schick ya fara cin kwallo a minti na 30, sai ya kara na biyu a minti biyu tsakani, sannan ya ci na uku da ka.

Victor Boniface ne ya ci wa Leverkusen kwallo na hudu a wasan, rabon da Bochum ta doke Leverkusen tun a kakar bara a cikin watan Mayu.

Kungiyar da Xabi Alonso ke jan ragama ta yi wasa 16 ba tare da rashin nasara ba a Bundesliga jimilla 24 a dukkan karawa, wadda ta ci wasa 21 da canjaras uku.

Bayern Munich mai kwantan wasa daya ta yi nasara a kan Wolfsburg da cin 2-1 ranar Laraba.

Jamal Musiala ne ya ci mata kwallon farko daga baya Harry Kane ya kara na biyu na 21 da ya zura a raga a bana a Bundesliga, bayan wasannin mako na 16.

Stuttgard ta koma ta ukun teburin, bayan doke Augsburg 3-0, ita kuwa Union Berlin cin Cologne 2-0 ta yi da wanda Heidenheim ta zura kwallo a ragar Freiburg daf da za a tashi wasa.

Ita kuwa Eintracht Frankfurt ta yi nasarar cin Borussia Munchengladbach 2-1.

Za a yi hutun mako uku da rabi daga nan a ci gaba da zagaye na biyu a Bundesliga.

Leave a comment