Lemma dan kasar Ethiopia ya lashe Valencia Marathon

Dan kasar Ethiopia, Sisay Lemma ya lashe gudun fanfalaki na Valencia ranar Lahadi.

Mai shekara 32 ya yi nasara cikin awa biyu da minti daya da dakika 48.

Kadan ya rage ya zarta bajintar da dan kasar Kenya Kelvin Kiptum ya yi, wanda ya lashe gasar Chicago cikin awa biyu da dakika 35.

Wadanda suke da tarihin kwazo fiye da Lemma kawo yanzu sun hada da Kiptum da Eliud Kipchoge (Berlin, 2022) da kuma Kenenisa Bekele (Berlin, 2019)

Lemma ya lashe gasar ta Valencia, yayin da dan kasar Kenya, Alexander Mutiso ya yin a biyu da kuma dan kasar Ethiopia Dawit Wolde na uku.

Wanda ya yin a hudu shi ne Bekele, mai shekara 41.

Leave a comment