Leipzig na son kammala Bundesliga a mataki na hudu

RB Leipzig na son kammala Bundesliga a mataki na hudu a kan teburi a kakar bana, duk da biyar ne daga Germanyu za su shiga Champions League a badi.

Leipzig, wadda za ta karbi bakuncin Borussia Dortmund ranar Asabar tana da maki 59 a mayaki na hudu da tazarar maki biyu tsakani da Dortmund, kuma saura wasa hudu a kammala kakar bana.

Kungiyoyin hudun farko ne a Bundesliga za su kai Champions League a badi kai tsaye, koda yake watakila biyar ne za su wakilci kasar a sabon fasalin da za a fara daga badi.

Leipzig, wadda za ta je Amurka atisayen tunkakar kakar badi cikin watan Agusta za ta kara da Aston Villa a New Jersey.

Tuni dai kungiyar Germany ta buga Champions League na bana, inda Real Madrid ta yi waje da ita a zagayen ‘yan 16 da cin kwallo 2-1 gida da waje.

Leipzig ta ce za ta rike ‘yan wasan da take da su, domin fuskantar kakar badi, bayan da ta sayar da Josko Gvardiol da Dominik Szoboszlai da Christopher Nkunku da kuma Konrad Laimer kan fara kakar nan.

Leave a comment