Leicester City ta koma gasar Premier League

Kungiyar Leicester City ta samu gurbin komawa buga Premier League daga kakar badi.

Ta samu wannan gurbin bayan da Queens Park Rangers ta doke Leeds United ranar Juma’a.

Kuma 4-0 da aka ci Leeds a Loftus Road na nufin kungiyar da Daniel Farke ke jan ragama tana ta biyun teburi da tazarar maki hudu tsakani da Leicester ta daya.

Leicester na shirin samun gurbin buga Premier League a badi, bayan da ta fado daga wasannin bara.

Leicester za ta iya lashe Championship ranar Litinin a gidan Preston idan har Ipswich wadda take ta ukun teburi ta kasa doke Hull City ranar Asabar.

Ipwich za ta bi sawun Leicester City zuwa Premier League a badi, idan za ta hada maki biyar daga wasa ukun da ke gabanta.

Leave a comment