Lebron james zai yi jinya a karon farko a nba a bana

LeBron James ba zai buga wa Los Angeles Lakers wasan da za ta karbi bakuncin Portland Trail Blazer a karshen mako ba.

Wasan farko da ba zai yi ba a gasar kwallon kwandon NBA ba, bayan da yake jinya.

James, mai shekara 38 ya ji rauni a zangon farko a wasan da Lakers ta yi nasara a kan Phoenix ranar Juma’a, bayan da ya yi karo da Kevin Durant.

Wanda ke buga kaka ta 21 a kwallon kwandon Amurka shi ne kan gaba a yawan hada maki da bayar da kwallo a ci.

Leave a comment