LeBron James ya zama na farko da ya ci maki 39,000 a NBA.

LeBron James ya zama dan wasa na farko da ya ci maki 39,000 a NBA yayin da LA Lakers ta doke Utah.

Yana buƙatar maki biyar amma ya zira kwallaye 17 a cikin nasaran 131-99 da Lakers suka samu, wanda ya tabbatar musu da matakin kusa da na karshe.

James, mai shekaru 38, ya zarce Kareem Abdul-Jabbar na LA LAKERS mai maki 38,387, Tun a watan Fabrairu, James ya zama dan wasan da ya fi zura kwallo a kwando a tarihin NBA.

Leave a comment