Joan Laporta ya kara lashe zaben shugaban Barcelona, zai kuma kara jan ragama kaka biyar nan gaba kamar yadda ƙungiyar ta sanar.
Zai fara aiki ranar 1 ga watan Yuli, kuma karo na hudu na biyu a jere da zai shugabanci ƙungiyar Camp nou, bayan da ya lashe zaben da kaso 68 cikin 100.
Mambobi da magoya baya kusan 48,500 suka kaɗa kuri’a, inda Laporta ya samu kuri’a 32,934, yayin da abokin takararasa Victor Font ya samu 14,385, kimanin kaso 30 cikin 100.
Laporta ya fara shugabantar Barcelona a 2003 zuwa 2010, kuma shi ne ya ɗauko Pep Guardiola da ya horar da ƙungiyar da ta kai ta kara samun nasarori da fito da kanta a Turai da duniya a fannin taka leda.
Barcelona ta yi fama da matsaloli da yawa da ta kusan durkushewa, amma a kakar da ta wuce ta lashe kofi uku da caskara Real Madrid a wasannin hamayya na El Clasico da suka yi.
Kawo yanzu Barcelona, wadda Hansi Flick ke jan ragama tana ta ɗaya a kan teburin La Liga da tazarar maki huɗu tsakani da Real Madrid ta biyu.
Barcelona za ta karɓi bakuncin Newcastle United a wasa na biyu a zagaye na biyu a Champions League ranar Laraba, bayan da suka tashi 1-1 a St James Park a makon jiya.