Labarun da suka shafi cinikin ‘yan kwallo

Kungiyoyi uku na son sayen Toney a karshen kakar nan

West Ham United za ta kalubalanci Arsenal da Chelsea kan daukar dan kwallon Brentford, Ivan Toney da zarar an kammala kakar bana.

Ronald Araujo ya fadi makomarsa a Barcelona

Mai tsaron bayan Barcelona, Ronald Araujo ya ce ya yanke shawarar ci gaba da taka leda a kungiyar, duk da rade-radin da ake cewar Bayern Munich da Manchester United na son yin zawarcinsa da zarar an karkare kakar nan.

Arsenal ‘na fatan riga Barcelona daukar Joao Cancelo ‘

Wasu rahotanni na cewar Arsenal za ta yi kokarin sayen dan wasan Manchester City, Joao Cancelo idan har Barcelona ba za ta iya daukar dan wasan ba.

Dan wasan Brighton & Hove Albion, Deniz Undav na son komawa Stuttgart

Deniz Undav ya nuna sha’awar barin Brighton & Hove Albion zuwa Stuttgart, kungiyar da ya ci wa kwallo 14 a wasa 22 a Bundesliga, wadda yake buga wa wasannin aro a kakar nan.

Arsenal da Tottenham na rige-rigen daukar dan wasan Barcelona’, Raphinha’

Kungiyar Saudi Arabia, Al-Hilal za ta taya dan wasan Barcelona, Raphinha kudi mai tsoka dan kwallon da Arsenal da kuma Tottenham ke rige-rigen saya a karshen kakar nan.

Wani dan wasan Real Madrid ya ce an kusan kammala cinikin Kylian Mbappe

Dan wasan Real Madrid,Aurelien Tchouameni ya bayar da hasken cewar takwaransa daga France, Kylian Mbappe zai kammala kulla yarjejeniyar komawa Santiago Bernabeu da zarar an gama kakar bana.

Arsenal za ta kalubalanci Tottenham wajen sayen dan kwallon Nottingham Forest kan £42m

Wani rahoto ya ce Arsenal za ta bi sawun Tottenham da West Ham United a kokarin sayen Morgan Gibbs-White bayan da Nottingham Forest ke fustankar matsin tattalin arziki.

Man City da Man United da Real Madrid na son daukar mai tsaron bayan kan £60m

Manchester United da Real Madrid za su fuskanci kalubale daga Manchester City kan sayen dan wasan Everton, mai tsaron baya, Jarrad Branthwaite, in ji wasu rahotanni.

Manchester United na shirin taya dan kwallon tawagar Spain daga Barcelona

Barcelona na shirin bai wa Pau Cubarsi mai shekara 17, sabon kwantiragi mai tsoka, bayan wasu rahotanni da ke cewar Manchester United za ta yi zawarcin an wasan da zarar an kammala kakar nan.

Manchester United za ta tura a je a kalli wasan matashin Barcelona mai darajar £25m

Manchester United za ta tura a je a kalli wasan matashin Barcelona, mai tsaron baya Mikayil Faye, wanda take fatan tuntuba da zarar an kare kakar nan.

Wani fitatcen dan kwallon Real Madrid na daf da tsawaita zanmansa a Santiago Bernabeu

An bayar da rahoton cewar dan wasan Real Madrid, Toni Kroos na daf da saka hannu kan yarjejeniyar kaka daya a Real Madrid, wanda kwantiraginsa zai kare a karshen kakar nan.

Manchester United ta yanke shawarar kan Sofyan Amrabat

Manchester United ba za ta dauki dan kwallon Fiorentina ba mai buga mata wasanni aro, Sofyan Amrabat koda an kammala kakar nan.

Leave a comment