Kuskuren da Arsenal ya sa Aston Villa ta doke ta a Emirates

Arsenal ta kasa amfana da damar da ta samu ta darewa kan teburin Premier League, bayan da Aston Villa ta doke ta 2-0 a wasan mako na 33 ranar Lahadi a Emirates.

Aston Villa, karkashin tsohon kociyan Gunners, Unai Emery ta ci kwallayen ta hannun Leon Bailey saura minti a tashi, sannan ta kara na biyun ta hannun Ollie Wwatkins saura minti uku alkalin wasan ya busa tashi,

Da wannan sakamakon Arsenal tana ta biyu a teburin Premier da tazarar maki biyu tsakaninta da Manchester City, wadda ta ci Luton 5-1 ranar Asabar.

‘Jerin Kurakuran da Arsenal ta yi a wasa da Aston Villa.

Ta saka masu cin kwalllo da yawa

Bayan da Mikel Arteta ya yanke shawara saka masu cin kwallo biyar daga gaba, hakan ya sa kungiyar an yi ta kai mata hare-hare.

Duk da cewar Aarsenal ce ta rike wasan kaso mai tsoka, amma ta kasa bayar da kwallayen da ya kamata ‘yan gaban su amfana.

Canja salon wasa

Amfani da tsohon dan kwallon Manchester City, Zinchenko ya yi amfani sosai, wanda ya dunga kula da gurbin Declan Rice idan ya kara yin sama.

Hakan ya hana Aston Villa sakat, wadda ta koma buga kwallo sama mai tsawo, hakn bai zama baraza na ga ‘yan bayan Arsenal, musammam Saliba da kuma Magalhaes.

Rashin hakurin Arsenal ya sa ta sauya salon wasan da ta fara tun farko, inda a zagaye na biyu Haverz ya kasa ratsa bayan Aston Villa balle ya ci kwallo.

Canji a kurarren lokaci

Dan jiran da Arteta ya yi domin canji da ya kamata ya kawo tsaiko a karawar ta ranar Lahadi, inda kungiyar ta yi ta kokarin ganin ta zura kwallo a ragar Aston Villa.

Duk da cewar ta saka Jorginho da Smith – Rowe, Gunners ta kasa samun damar zura kwallo a raga, wadda daf da za a tashi ta yi sakacin da aka zuba mata biyu a raga.

Sauwa wasa shida Gunners ta kare wasannin Premier League daga ciki za ta fuskanci Chelsea da Manchester United da Tottenham.

Ranar Laraba Arsenal za ta je Bayern Munich domin buga wasa na biyu a Champions League zagayen quarter finals, bayan da suka tashi 2-2 a Emirates ranar Talata.

Leave a comment