An kusan fara gasar cin kofin nahiyar Turai karo na 17, wato Euro 2024, inda German za ta karbi bakuncin wasannin bana da za ta kara tsakanin tawaga 23.
Za a fara bude labulen gasar daga 14 ga watan Yuni zuwa 14 ga wayan Yuli, inda za a yi wasa 51 har da 36 a cikin rukuni, inda za a fitar da 16 da za su ci gaba da wasannin zagaye na biyu.
Cikin wasannin da za a fara, za a samu wadda za ta lashe kofin bana da ake kira Henri Delaunay Cup a filin wasa na Olympiastadion a Berlin.
Tuni hukumar kwallon kafa ta Turai ta sanar a cikin Disambar bara cewar za ta raba £282.87m tsakanin tawagogin da za su buga gasar bana, iri daya da yadda aka raba a Euro 2020.
Dukkan kungiyar da ta samu gurbin shiga Euro 2024 su 24, kowacce za ta karbi £7.93m tun kan fara taka leda.
Akwai ladan cin wasa a cikin rukuni £860,000, sannan a biya £429,000 idan aka yi canjaras, ba kudin da za a bai wa tawaga idan an doke ta a wasa.
Dukkan tawagar da ta kai zagaye na biyu na ‘yan 16, kowacce za ta karbi £1.29m, sannan a bayar da £2.14m ga kwata fainals da kuma £3.43m ga wadda ta kai daf da karshe .
Duk wadda ta lashe Euro 2024 za ta karbi ladan £6.86m, wadda aka doke a wasan karshe ta karbi £4.29m.
Kudin da tawaga za ta lashe har zuwa daukar kofin ya kai £24.23m.