Koronabirus ya yi tashe tsakanin sa’oinsa a damben gargajiya

Ɗan wasan damben gargajiya da ake kira, Koronabirus ya taka rawar gani tsakanin abokan wasansa ya kuma yi suna ya samu alheri da yawa.

Koronabirus yana bugu da hannun dama kuma Bakude, wanda ya fara wasa cikin farin jinin magoya baya, ganin yadda yake sa ƙwazo da himma a lokacin da yake wasansa.

Ya samu sunan Koronabirus daga wajen Mamman Bashar Danliti, sakamakon da cutar da ta ɓulla a duniya da ta kawo koma baya a fannin rayuwa da sauran batutuwa a duniya.

Kenan matashin ɗan wasan ya fara dambe a filin wasa da ke Ado Bayero Square a Kano, Nigeria daga nan ya yi suna ya fara fita sauran gidajen wasa, domin nuna jarumtar da yake da ita.

Daga nan sunansa ya fara faɗada musamman a Marabar Nyanya gidan Idris Umar Ɓanɓarewa, inda duk mako ake sa masa damben gasa tsakani da matasa daidai shi.

Haka kuma Korona sai ya fito da yin wasa uku a rana ɗaya ko fiye da haka, saboda haka da zarar an ganshi a fili, ana sa zan zai buga wasa da dama

Shi dai Koronabirus Shagon Alin Bata isarka ne – tsohon dan dambe da har yanzu yana yin wasan, koda yake sa’anninsa ba su da yawa a yanzu haka.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top