Kocin Milan ya fadi dalilin da ya ajiye Chukwueze a benci

Mai horar da AC milan, Stefano Pioli ya fadi dalilin da ya ajiye Samuel Chukwueze a benci a wasan Juventus a gasar Serie A.

Juventus, wadda ta karbi bakuncin AC Milan ranar Asabar 27 ga watan Afirilu sun tashi 0-0 a wasan mako na 34 a gasar Serie A, wadda tuni Inter Milan ta dauki kofin bana.

Chukwueze, wanda ke taka rawar gani a wasannin da yake buga wa, an yi mamaki da aka ganshi a kan benci a fafatawa da Juventus ranar Asabar.

Daga baya an saka dan kwallon tawagar Nigeria a wasan, wanda ya canji Christian Pulisic saura minti bakwai a tashi daga fafatawar.

Tun daga lokacin aka ta caccakar Pioli kan shawarar da ya yanke ta fara wasa da dan kwallon tawagar Super Eagles a kan benci.

Kociyan ya ce dalilin ya zabi ya saka mai cin kwallo, maimakon mai buga wasa daga gefe domin su kai hare-hare da yawa a karawar da suka raba maki a babbar gasar tamaula ta Italy.

Mai shekara 24 ya ci kwallo daya a wasa 22 a lik da ya buga wa Milan a kakar nan.

Leave a comment