Kocin Milan Pioli ya ce zai takawa Inter burki

Kocin AC Milan, Stefano Pioli na fatan doke Inter Milan kan dalilai da yawa a wasan mako na 34 za su kara a Serie A ranar Litinin.

An yi wa da Milan a Europa League ranar Alhamis a hannun Roma mai buga Serie A, kenan kungiyar da koci Pioli ke jan ragama na fatan taka rawar gani a wasan hamayya da Inter a San Siro.

Milan wadda take ta biyu teburi a wasan da za su kara ranar Litinin, wanda Inter ke jan ragama za ta dauki Serie A na bana, ida ta ci Milan, abinda Pioli ke fatan sai dai a wasa na gaba ba dai a kansu ba.

Muna fatan yin abin kirki in ji Pioli, wanda ya kara da cewar ”Saboda an fitar da mu a Europa League, sannan abokiyar hamayya na fatan lashe Scudetto a kanmu, kenan wannan karawar tana da muhimmaci idan muka ci wasan.”

”Na yadda da ‘yan sana na, sun kwan da sanin mahimmacin wasan nan.Mun san cewar idan muka sa kwazo ba tare da barar da damar-maki ba, sannan ba mu bari Inter ta wala kamar yadda suka yi a wasan baya, lallai za mu iya samun maki.”

Milan na fatan rama doke ta 5-1 da aka yi a wasan farko a bana da fara Serie A, lokacin Inter na kan ganiya, wadda ta yi nasara biyar baya a kan Milan a fafatawar hamayya da suka buga.

Haka kuma Pioli ya kwan da sanin suna bukatar sa kwazon da ya dace, idan har suna son cin Inter ranar Litinin.

Idan Milan ta yi nasara a karawar ta samu gurbin shiga Champions League na badi tun kan kammala Serie A ta kakar nan.

Leave a comment