Kobe ta lashe kofin Japan wata biyar bayan barin Iniesta

A karon farko Vissel Kobe ta lashe kofin Japan ranar Asabar, wata biyar tsakani da Andres Iniesta ya bar kungiyar.

Kobe ta doke Nagoya Grampus 2-1 ta dauki babban kofin gasar tamuala na Japan, saura wasa daya a rufe kakar bana.

Iniesta ya koma Kobe a 2018, bayan barin Barcelona, wadda ya yiwa wasa sama da 600 da lashe Champions League hudu da La Liga tara.

Mai shekara 39, wanda ya lashe kofin duniya da Spain a 2010 ya bar kungiyar Japan cikin watan Yuli, wanda ya koma Emirates FC.

Mi rike da kofin bara, Yokohama canjaras ta yi, hakan ya sa Kobe ta lashe kofin kakar bana.

A bara Kobe ta yi zaman teburin karshe kafin daga baya ta karkare a mataki na 13 a gasar da kungiyoyi 18 ke fafatawa.

Kungiyar ta koma kan ganiya bayan da Yoshida ya ajiye Inesta a benci, wanda ya yi wasa hudu daga nan ya bar Kobe tana ta ukun teburi.

Juan Mata ya koma kungiyar ta Japan a cikin watan Satumba, amma wasa daya kacal ya buga kawo yanzu.

Kobe ta lashe Emperor’s Cup da Iniesta a 2019 da kai wa daf da karshe a Asian Champions League a bara.

Iniesta ya taka leda a Kobe tare da David Villa dakuma Lukas Podolski a kungiyar da attajiri, Hiroshi Mikitani ya mallaka.

Leave a comment