Kocin Manchester United. Michael Carrick, ya bayyana cewa za su na iya neman ɗan wasan gaba mai buga gefen hagu a kasuwar saye da sayarwa ta bazara.
A halin yanzu, Matheus Cunha ne kaɗai zabin da United ke da shi a bangaren hagu, bayan da Patrick Dorgu ya ji rauni. Amad Diallo ya taba taka rawar gani a wannan bangare, amma ya fi kwarewa a gefen dama.
A baya-bayan nan United na da yawan ƴan wasan da ke taka leda daga hagu, amma yanzu ta samu giɓi bayan sayar da Alejandro Garnacho tare da bayar da aron Marcus Rashford da Jadon Sancho.
Rahotanni na nuna cewa Rashford da Sancho ba za su sake komawa Old Trafford ba, idan yarjejeniyar da suke buga wasannin aro ta kare.
