Ko Salah zai kafa tarihi biyu a fannin cin Man United kwallaye?

Manchester United za ta karbi bakuncin Liverpool a wasan mako na 32 a Premier League ranar Lahadi a Old Trafford.

Aranar ce Mohammed Salah zai yi fatan kafa tarihi biyu a cin Manchester United kwallaye a Premier Leahue.

Kungiyar Anfield ita ce ta daya a kan teburin Premier League da tazarar maki biyu tsakaninta da Arsenal da tazarar uku tsakani da Manchester City mai rike da kofin bara.

Rabon da a doke Liverpool a lik tun bayan rashin nasara a hannun Arsenal cikin watan Fabrairu, kenan karawa bakwai ba a yi nasara a kanta ba.

To sai dai Liverpool mai fatan daukar kofi hudu a bana, bayan lashe League Cup, United ta fitar da ita a FA Cup da cin 4-3.

Salah yana daga cikin ‘yan wasan Liverpool da suka ci mata kwallo kuma na 13 da ya ci United a wasa 14 a dukkan fafatawa.

Kawo yanzu Salah ya ci wa Liverpool kwallo 22 ya bayar da 13 aka zura a raga a wasa 34 a dukkan fafatawa a bana.

Tarihi biyu da Salah ke fatan kafawa a kan United a Premier League

Salah na fatan cin United kwallo karo hudu a jere a Old Trafford, bayan da ya ci uku a babbar gasar tamaula ta Ingila, kenan babu mai wannan bajintar.

Salah ya zura kwallo 10 a ragar United a Premier League, wanda ya yi kan-kan-kan da Alan Shearer. Shin ko Salah zai zama kan gaba a yawan cin United daga ranar Lahadi.

Leave a comment