Ko Real za ta kai kwata fainal a Etihad a Champions League?

Manchester City za ta karɓi bakuncin Real Madrid ranar Talata a wasa na biyu a Champions League, domin neman gurbin kwata fainals.

A makon da ya wuce ranar Laraba ƙungiyar Sifaniya ta doke ta Ingila da cin 3-0 a wasan farko da suka buga a Santiago Bernabeu.

Real Madrid ta ci ƙwallayen uku rigis ta hannun Federico Valverde da hakan ya sa kafarta ɗaya ta fara jin ƙanshin zagayen ƴan 16 a gasar zakarun Turai.

Wannan shi ne wasa na biyu a bana da za su buga a tsakaninsu, bayan da City ta je ta doke Real 2-1 ranar 10 ga watan Disambar 2025.

Kuma karo na 17 da za su fuskanci juna a dukkan fafatawa a gasar zakarun turai, inda Real Madrid ta yi nasara shida da canjaras biyar, City ta ci karawa biyar daga ciki.

City tana mataki na biyu a teburin Premier League da tazarar maki tara tsakani da Arsenal ta ɗaya, itama Real tana ta biyu a teburin La Liga, amma da tazarar maki huɗu tsakani da Barcelona mai jan ragama.

Ƴan wasan Real Madrid da suka je Etihad:


Masu tsare raga: Courtois, Lunin da kuma Fran González.
Masu tsare baya: Carvajal, Alaba, Trent, Carreras, Fran García, Rüdiger, Huijsen, Diego Aguado da kuma Mario Rivas.
Masu buga tsakiya: Bellingham, Camavinga, Valverde, Tchouameni, Arda Güler, Cestero, Manuel Ángel, Palacios da kuma Thiago.
Masu cin ƙwallaye: Vini Jr., Mbappé, Gonzalo, Brahim da kuma Mastantuono.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top