Ko PSG za ta fitar da Barcelona a Champions League?

Barcelona ta karbi bakuncin Paris St Germain domin buga wasa na biyu a zagayen quarter finals a Champions League da za su kara ranar Talata a Spain.

Ranar Laraba 10 ga watan Afirilu, Barca ta je ta ci PSG 3-2 a wasan farko a France, inda Raphinha ya ci mata biyu da Andreas Christensen ya zura daya a raga, yayin da Ousmane Dembe da Vitinha suka ci wa PSG kwallaye.

Wannan shi ne karo na 15 da za su fuskanci juna a gasar zakarun Turai, inda Barcelona ta ci wasa shida da canjaras hudu, PSG ta ci karawa hudu.

Ranar Asabar Barcelona ta je ta ci Cadiz 1-0 a wasan mako na 31 a La Liga, ita kuwa PSG ba ta buga Ligue 1 ba a karshen mako, domin ta samu hutun da zai ba ta damar taka rawar gani a Spain a wasan neman zuwa daf da karshe.

Barcelona za ta buga wasan hamayya na El Clasico da Real Madrid da zarar ta kammala da kungiyar France, PSG kuwa za ta karbi bakuncin Lyon a karawa mai zafi nan gaba idan ta koma gida bayan gasar zakarun Turai.

Tsohon dan kwallon Barcelona, wanda ya yi mata koci a baya, Luis Enrique ne ke jan ragamar Paris St Germain, kenan ya kwan da sanin cewar akwai jan aiki a gabansu a wasa na biyu a Spain.

A kakar 2015 Enrique ya lashe kofi uku a Barcelona, mai shekara 53 ya yi kaka takwas a matakin dan wasa a Barca, sannan ya horar da kungiyar tsakanin 2014 zuwa

Haka shima Xavi tsohon dan kwallon Barca ne wanda ya lashe kofi sama da 20 a kungiyar, sannan ya ja ragamar daukar La Liga a bara a matakinsa na mai horar da kungiyar.

Xavi ya buga wa Barca wasa sama da 500, sannan ya yi ritaya a matakin koci a Nuwambar 2021, amma ya sanar zai yi ritaya a karshen kakar nan.

PSG ba ta taba daukar Champions League ba, yayin da Barcelona take da biyar jimilla, amma rabon da ta dauka tun 2014/15.

Leave a comment