Ko Plateau United za ta samu maki kan Tornadoes?

A karshen mako za a ci gaba da wasannin mako na 29 a gasar Premier ta Najeriya da za a buga wasa da yawa a faɗin kasar.

Plataeu United tana daga cikin ƙungiyoyin da za su fafata, wadda za ta karɓi bakuncin Niger Tornadoes.

Wasan farko da suka buga a jihar Niger a cikin watan Oktoba, Plateau United ta sha kashi 4-0.

Ita dai Plateau tana ta 12 a teburi da maki 36 a wasa 38, Tornadoes kuwa karawa 37 ta yi tana ta 13 da maki 37, ƙenan maki ɗaya ne a tsakaninsu.

A makon da ya gabata, Plateau ta yi rashin nasara 2-1 a hannun Barau FC a filin wasa na Sani Abach da ke Kofar Mata a jihar Kano.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top