Ko Milan za ta kai zagayen gaba a Champions League?

AC Milan za ta karbi bakuncin Borussia Dortmund a wasa na biyar-biyar a cikin rukuni a Champions League ranar Talata.

Kungiyar Italy ta je ta tashi 0-0 a wasa na bibiyu a cikin rukuni cikin Oktoba a Jamus.

Wannan shi ne karo na takwas da za su kece raini a tsakaninsu, inda Milan ta ci uku da canjaras biyu, Dortmund ta yi nasara a biyu.

Kungiyar Italy ta samu damar nan, bayan da ta ci PSG a wasa na hurhudu a cikin rukuni na shida.

Milan wadda ta taka rawar gani a Champions League a bara tana ta ukun teburi da maki biyar.

Dortmund ce ta daya mai maki bakwai, sai PSG mai maki shida ta biyu.

Newcastle, mai maki hudu ta karshen teburi za ta kara da PSG ranar Talata a Faransa.

Wasannin da za a buga ranar Talata:

  • Lazio da Celtic
  • Shakhtar Donetsk da Royal Antwerp
  • Manchester City da RB Leipzig       
  • AC Milan da Borussia Dortmund
  • Feyenoord da Atletico Madrid       
  • FC Barcelona da FC Porto       
  • Paris Saint-Germain da Newcastle United        
  • Young Boys da Crvena Zvezda

Leave a comment