Ko mbappe zai koma Real Madrid a Janairu?

Har yanzu ba a san halin da ake ciki ba kan batun komawar Kylian Mbappe zuwa Real Madrid ba.

Dan kwallon tawagar Faransa yana da sauran yarjejeniyar kaka daya a Paris St Germain, wanda ya shirya zuwa Real Madrid a karshen kakar nan.

Daga baya an sasanta da dan wasan, wanda aka daina saka shi a atisaye, yanzu shi ne kan gaba a cin kwallaye a Ligue 1 mai 13 a raga.

Getafe na son tsawaita yarjejeniyar Mason Greenwoord da ke buga mata wasannin aro daga Manchester United. (Sun)

Manchester City na son daukar dan wasan Chelsea, Reece James, domin maye gurbin Kyle Walker, mai shekara 33. (Independent, via Manchester Evening News)

An bukaci Liverpool ko kuma Tottenham su biya fam miliyan 30 ga duk wadda ke son sayen dan kwallon Bournemouth, Lloyd Kelly a watan Janairu idan an bude kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallo a Turai. (Football Insider)

Inter Milan na son daukar dan wasan Borussia Monchenglad, Winsley Boteli, wanda Everton ta dade tana zawarci. (Inter Milan Live via Liverpool Echo)

Barcelona na sha’awar daukar dan wasan tawagar Najeriya, Wilfred Ndidi, amma sai yarjejeniyarsa ta kare da Leicester City a karshen kakar nan. (Sky Sports)

Har yanzu Real Madrid na fatan daukar dan kwallon Bayern Munich, Alphonso Davies da zarar an kammala kakar bana. (Fabrizio Romano)

Leave a comment