Ko Manchester United za ta dauki fansa a kan Bournemouth kuwa?

Manchester United ta je Bournmouth domin buga wasan mako na 33 a Premier League da za su kara ranar Asabar.

Kungiyoyin biyu sun kara ranar 9 ga watan Disambar 2023 a Old Trafford, inda Bournemouth ta ci 3-0, kuma wadanda suka ci mata kwallayen sun hada da Dominic Solanke da Philip Billing da kuma Marcos Senesi.

Kungiyar da Erik Ten Hag ke jan ragama tana ta shidan teburi da maki 49, ita kuwa Bournemouth mai maki 41 tana ta 12.

Bayanai kan lafiyar ‘yan wasa

Bournemouth za ta buga wasan ba tare da Antoine Semenyo da Marcus Tavernier, wadanda suka ji rauni a karawa da Luton.

Chris Mepham ya kamu da rashin lafiya, wadanda ke jinya sun hada da Tyler Adams da Ryan Fredericks da kuma Luis Sinisterra.

Manchester United na auna koshin lafiyar, Marcus Rashford wanda aka sauya shi a karawa da Liverpool.

Masu jinya a United sun hada da Scott McTominay da Raphael Varane da kuma Jonny Evans.

Bayanai kan haduwa tsakanin kungiyoyin

Manchester United ta ci wasa hudu baya a Premier League da ta je gidan Bournemouth har da 1-0 da ta yi nasara a bara.

Bournrmouth na fatan doke United gida da waje a karon farko a lik a tarihi.

Kungiyar Bournemouth

Bournemouth na fatan cin wasa hudu a jere a Premier League a karon farko a tarihi.

Wasa biyu kungiyar ta yi rashin nasara daga 11 a gida da cin shida da canjaras uku, inda Liverpool da Manchester City ne suka doke ta.

Dominic Solanke na bukatar cin kwallo daya domin ya zama 17 da ya ci a Premier League na farko mai wannan bajintar a kaka daya, yanzu yana da 16 a raga, ya yi kan-kan-kan da Joshua King a 2016/17.

Kungiyar Manchester United

Manchester United ba ta ci wasa ba daga uku da ta kara a baya a waje a Premier League da canjaras daya ta yi rashin nasara biyu.

An ci United kwallo 17 da ake zura mata a raga a karawa takwas a lik tun bayan da ta tashi 0-0 a Anfield cikin Disamba.

United ta barar da maki 15 da ya kamata ta lashe a wasannin kakar nan.

Diogo Dalot na daf da buga wasa 100 a Premier League, zai zama na hudu daga Portugal da ya yi karawa da yawa a babbar gasar tamaula ta Ingila, bayan Cristiano Ronaldo da Bruno Fernandes da kuma Nani.

Wasannin mako na 33 a Premier League

  • Newcastle United da Tottenham
  • Brentford da Sheffield United   
  • Burnley da Brighton
  • Manchester City da Luton Town             
  • Nottingham Forest da Wolverhampton
  • Bournemouth da Manchester United

Leave a comment