Ko Manchester City za ta lashe kofi na biyar a 2023?

Za a buga wasan karshe a gasar kofin duniya ta zakarun nahiyoyi da ake buga wa a Saudi Arabia ranar Juma’a.

Za a fafata ne tsakanin Manchester City mai rike da kofin zakarun Turai da Fluminense mai rike da kofin zakarun Kudancin Amuraka.

Pep Guardiola ya sanar da ‘yan wasansa cewar idan suka lashe kofin zai zama bajinta da tarihin da ba za su taba mantawa ba a duniya.

To sai dai City wasa daya ta ci daga shida baya, kafin ta ziyarci Saudi Arabia, amma cikin ruwan sanyi ta doke Urawa Red Diamonds 3-0 ta kuma kai zagayen karshe.

Ana hasashen cewar kungiyar Etihad ce za ta dauki kofi na biyar a shekarar 2023 idan ka hada lissafi da Champions League da Premier League da Fa Cup da Uefa Super Cup.

Tun daga 2012 kungiyoyin nahiyar Turai ne ke lashe Fifa Club World Cup a tarihi.

Kafin wasan karshe din, za a fara karawar neman mataki na uku tsakanin Urawa Red Diamonds ta Japan mai rike da kofin zakarun Asia da Al Ahly ta Masar mai kofin zakarun Turai.

Man City ce ta doke Red Didomds a wasan daf da karshe, ita kuwa AlAhly rashin nasara ta yi a hannun Fluminense ta Brazil mai rike da kofin zakarun Kudancin Amurak.

Za a buga fafatawar a filin wasa da ake kira Yarima Abdullah Al-Faisal da ke Jeddah a Saudi Arabia.

Leave a comment