Ko Man United za ta samu shiga gurbin zakarun Turai

Manchester United za ta karbi bakuncin Newcastle United a kwantan wasan mako na 34 a Premier League ranar Laraba a Old Trafford.

United mai maki 54 tana ta takwas din teburi, ita kuwa Newcastle United mai maki 57 tana ta shidan teburi da maki iri daya da na Chelsea, wadda take ta bakwai.

Wannan shi ne karo na uku da za su kara a bana a tsakaninsu, bayan da kungiyar St James Park ta je ta fitar da United a Old Trafford da cin 3-0 a League Cup cikin Nuwamba.

Haka kuma sun hada a St James Park a cikin Disamba a gasar Premier League, inda aka ci United 1-0., inda Newcastle ta karbi bakunci.

United, wadda ke fama da ‘yan wasa da yawa dake jinya, musamman daga baya ta yi rashin nasara biyu a jere a Premier League, inda Crystal Palace da Arsenal suka yi nasara a kanta.

Ana sa ran mai tsaron baya, Lisandro Martinez zai koma buga wa United, wanda ya yi mako shida yana jinya.

Haka kuma United tana auna koshin lafiyar Bruno Fernandes da Marcus Rashford da kuma Willy Kambwala.

Itama Newcastle za ta uana koshin lafiyar Alexander Isak, wanda aka sauya shi a karawa da Brighton da suka tashi 1-1, wanda ya kamu da rashin lafiya.

Da kyar idan Nick Pope zai iya buga wasan, amma Kieran Trippier da Joelinton da kuma Miguel Almiron duk sun murmure wadanda suka sha jinya.

Newcastle United, wadda Eddie Howe ke jan ragama ta samu nasara a wasa uku baya da suka kara a dukkan haduwa.

Watakila Newcastle ta ci United gida da waje a karon farko tun bayan 1930-31..

Leave a comment