Ko Man United za ta koma ta shida a Premier League?

Crystal Palace da Manchester United za su buga wasan mako na 36 a Premier League ranar Litinin a Selhurst Park.

Wannan shi ne karo na uku da za su kara a bana, inda United ta ci 3-0 a League Cup, yayin da Palace ta yi nasara 1-0 a Premier League.

Tuni dai United ta koma ta takwas da maki 54 iri daya da na Chelsea, wadda take ta bakwai, bayan da ta casa West Ham 5-0 ranar Lahadi.

Ita kuwa Palace mai maki 40 tana ta 14 a teburin Premier League, ba ta fuskantar barazanar ficewa daga gasar bana.

Palace na fatan doke United gida da waje a kan Manchester United a karon farko a tarihin Premier League.

Sai dai kwallo daya kacal United ta zura a ragar Place a wasa uku baya da ta je Selhurst Park.

Watakila mai tsaron bayan Palace, Marc Guehi ya buga wasan wanda ya ji rauni a gwiwa da ya yi jinyar wata biyu.

To sai dai kuma Eberechi Eze na jinya ba zai buga wa Palace wasan ba.

Ana tantama kan koshin lafiyar kyaftin din United, Bruno Fernandes, shi kuwa Harry Maguire zai yi jinyar mako uku,

Yayin da ake auna koshin lafiyar Scott McTominay, Jonny Evans da Anthony Martial sun warke, sai dai har yanzu Marcus Rashford na jinya.

Leave a comment