Ko Liverpool za ta kai zagayen gaba a Europa League?

Atalanta za ta karbi bakuncin Liverpool a wasa na biyu zagayen quarter finals ranar Alhamis a Europa League.

A makon jiya Atalanta ta je ta doke Liverpool a Anfield da cin 3-0, inda Gianluca Scamacca ya ci biyu, sannn Mario Pasalic ya zura na uku a raga.

Liverpool ta yi kaurin sunan wajen idan an doke ta wasan farko daga baya ta je ta farke ta kuma kai zagayen gaba, sai dai kamar wannan lokacin yanayin da ban yake da na baya.

Ranar Lahadi ta bari Crystal Palace ta doke ta 1-0 a wasan Premier League karawar mako na 33 a Anfield, hakan ya sa kungiyar ta kasa hawa kan teburin Premier League.

Yanzu Manchester City ce ta daya da tazarar maki biyu tsakaninta da Liverpool, bayan da ta shararawa Luton Town 5-1 ranar Asabar a babbar gasar tamaula ta England.

Arsenal ce ta biyu a kan teburi da maki 71 iri daya da na Liverpool ta uku, kuma saura wasa shida suka rage su karkare kakar bana.

Tuni kuma aka yi waje da Liverpool daga FA Cup na bana, bayan da Manchester United ta yi nasara da cin 4-3 a Old Traford.

Kawo yanzu Liverpool ta lashe Carabao daga kofi hudun da ta so dauka a bana, domin taya Jurgen Klopp murna wanda zai ajiye aikin horar da kungiyar a karshen kakar nan.

Sauran wasa shida a gaban Liverpool kan a karkare Premier League, ciki za ta fafata da Fulham da Everton da West Ham da Tottenham da Aston Villa da kuma Wolverhapton.

Kenan Liverpool na fatan lashe Premier League na bana da kuma Europa League idan ta doke Atalanta 4-0 ko 3-0 sannan su je karin lokaci zuwa bugun fenariti, Komai na iya faruwa a fannin Kwallon kafa.

Leave a comment