Liverpool za ta iya daukar wani kofin bayan Carabao a bana?

Liverpool ta barar da damar hawa kan teburin Premier League, bayan da Crystal Palace ta doke ta 1-0 ranar Lahadi a Anfield.

Kungiyar dake Selhurst Park ta ci kwallon ta hannun Eberechi Eze a minti na 14 da take leda, haka aka tashi ba tare da Liverpool ta farke ba.

Wasa na tara kenan da ake zura kwallo a ragar Liverpool a Premier League, inda hakan baraza na ce a fatan da take na daukar Premier League a kakar nan.

Kungiyar Anfield ta koma ta ukun teburi da maki 71 iri daya da na Arsenal, bayan da Manchester City ta dare kan teburin da maki 73.

Tun farko Liverpool wadda ta dauki Carabao Cup a bana ta sa ran lashe kofi hudu a kakar nan, domin taya murnar aikin da Jurgen Klopp ya gudanar, wanda ya sanar zai ajiye aikin a karshen kakar bana, yana bukatar hutu.

To sai dai Manchester United ce ta fitar da Liverpool a FA Cup na bana da cin 4-3 a zagayen daf da na kusa da na karshe, sannan Atalanta ta doke Liverpool 3-0 a Anfield a wasan farko a Europa League ranar Alhamis 11 ga watan Afirilu.

Liverpool za ta ziyarci Atalanta ranar Aalhamis 18 ga watan Afirilu, domin buga wasan neman kai wa zagayen daf da karshe a Europa League na kakar nan.

Haka kuma Liverpool, wadda ke mataki na uku a teburin Premier League, wadda saura wasa shida ta kammala babbar gasar tamaula ta England tana da wasu fafatawar masu zafi.

Cikin wasannin Premier League da za ta fuskanta har da wasan hamayya na Mersyside Derby da Everton da wanda za ta yi da West Ham da Tottenham da Aston Villa da kuma Wwolverhampton.

Wasannin dake gaban Liverpool:

Europa League Alhamis 18 ga watan Afirilu

  • Atalanta da Liverpool          

Premier League Asabar 21 ga watan Afirilu        

  • Fulham da Liverpool         

Premier League Laraba 24 ga watan Afirilu

  • Everton da Liverpool           

Premier League Asabar 27 ga watan Afirilu           

  • West Ham da Liverpool           

Premier League Lahadi 5 ga watan Mayu

  • Liverpool da Tottenham        

Premier League Litinin 13 ga watan Mayu              

  • Aston Villa da Liverpool           

Premier League Lahadi 19 ga watan Mayu

  • Liverpool da Wolves

Leave a comment