Liverpool za ta kara da Galatasaray ranar Laraba a wasa na biyu a Champions League a Anfield.
Wasan farko ƙungiyar Turkiya ta doke ta Ingila 1-0 ranar Talata 10 ga watan Maris, kuma karo na biyu da Galatasaray ta yi nasara a kan Liverpool a bana a gasar.
Liverpool ta sha kashi 1-0 a Turkiya a Champions League a hannun Galatasaray ranar Talata 30 ga watan Satumba.
Kenan Liverpool na bukatar ɗaukar fansa a kan Galatasaray ranar Laraba, domin ta kai zagayen kwata fainal a Champions League na kakar nan.
Wasa ɗaya Galatasaray ta ci daga 12 da ta ziyarci ƙungiyoyin Ingila a dukkan fafatawa da canjaras uku aka doke ta takwas daga ciki.
Wannan ɗayan da ta yi nasara shi ne cin Manchester United 3-2 a cikin Oktoban 2023.
Liverpool, wadda take ta biyar a teburin Premier League da maki 49 za ta je gidan Brighton ranar Asabar da zarar ta kammala wannan wasan..
Ita kuwa Galatasaray, mai jan ragamar gasar Turkiya da maki 64, za ta fafata da Trabzonspor a dai ranar ta Asabar.