Ko Juventus za ta lashe Copa Italia na 15?

Atalanta da Juventus za su kara a wasan karshe a Copa Italia ranar Laraba a Stadio Olimpico

Atalanta ta kawo wannan matakin bayan da ta doke Fiorentina 4-2 gida waje, kafin nan Juventus ta doke Roma 3-2 a wasa biyun da suka kara a gasar.

Wannan shi ne wasa na uku da za su fafata a bana, bayan da suka fara tashi ba ci a Serie A da aka buga a gidan Atalanta, wasa na biyu kuwa 2-2 suka tashi a Juventus.

Haka kuma a kan teburin Serie A, Juventus ce ta hudu, yayin da Atalanta take ta biyar, wadda za ta buga wasan karshe a Europa League da Bayern Leverkusen, wadda ta yi wasa 50 a jere ba a doke ta a dukkan fafatawa.

Juventus ce kan gaba a yawan lashe Copa Italia mai 14 jmilla, Atalanta guda daya ne da ita da ta lashe 1962/63.

Leave a comment