Ko Girona za ta koma matakin farko a La Liga?

Barcelona za ta karbi bakuncin Girona a karashen wasan mako na 16 a La Liga ranar Lahadi.

Kungiyoyin sun kara a bara, inda Barcelona ta je gidan Girona ta ci 1-0 ranar 28 ga watan Janairun 2023.

A wasa na biyu kuwa a gidan Barcelona ranar 10 ga watan ga watan Afirulun 2023 sun tashi 0-0 ne.

Girona mai maki 38 tana ta biyu a teburin La Liga, yayin da Barcelona tana mataki na uku da maki 34.

A ranar Asabar Real Madrid ta je ta tashi 1-1 a gidan Real Betis, hakan ya sa take da maki 39.

Jude Bellingham ne ya ci wa Real Madrid kwallon, kuma na 12 a LaLiga a kakar nan.

Wasannin da za a buga ranar Lahadi a La Liga:

  • Atletico Madrid da Almeria    
  • Granada da Athletic Bilbao    
  • Cadiz da Osasuna   
  • Barcelona da Girona

Leave a comment