Ko Falcons za ta rike tarihin rashin nasara a Banyana Banyana?

Tawagar kwallon kafa ta mata ta Nigeria ta ziyarci Africa ta Kudu, domin buga wasa na biyu na neman shiga gasar Olympic ranar Talata da birnin Paris zai karbi bakuncin kakar bana.

Ranar Juma’a suka buga wasan farko a Abuja, Nigetia, inda Super Falcons ta yi nasarar cin Banyana Banyana 1-0.

Super Falcon za ta kara da Banyana Banyana a Pretoria, wadda ta kwan da sanin ba ta taba rashin nasara ba a South Africa a babbar haduwa a tawagar mata a tsakaninsu.

Tazarar nasarar da Nigeria ta yi tana da yawa har da ranar 19 ga watan Maris 1995, inda Super Falcons ta ci 7-1 a wasan neman gurbin shiga gasar kofin duniya a 1995 a gaban ‘yan kallon South Africa.

Kenan har yanzu Banyana Banyana na fatan ganin ranar da ta doke Super Falcons a South Africa a fannin kwallon kafar mata.

Cikin wasa 24 baya da suka kara an buga bakwai a South Africa, inda Super Falcons ta lashe 15 daga ciki da canjaras biyar, inda ta yi rashin nasara hudu.

A karawa bakwai baya a South Africa, Nigeria ta yi nasara biyar da canjaras biyu.

Banyana Banyana da Super Falcons za su fafata a South Africa da karfe 6.30pm agogon Nigeria.

Tarihin karawa tsakanin Super Falcons da Banyana Banyana

4 Mar 1995: Nigeria 4 South Africa 1 (WCq)

19 Mar 1995: South Africa 1 Nigeria 7 (WCq)

25 Nov 2000: South Africa 0 Nigeria 2 (WAfcon)

18 Dec 2002: Nigeria 5 South Africa 0 (WAfcon)

30 Mar 2003: South Africa 0 Nigeria 3 (Friendly)

11 Oct 2003: Nigeria 1 South Africa 0 (AfGames)

12 Mar 2004: South Africa 2 Nigeria 2 (Oq)

28 Mar 2004: Nigeria 1 South Africa 0 (Oq)

9 July 2007: South Africa 2 Nigeria 2 (AfGames)

18 July 2007: South Africa 0 Nigeria 4 (AfGames)

28 July 2008: Nigeria 5 South Africa 0 (Oq)

12 Aug 2008: South Africa 0 Nigeria 1 (Oq)

22 Nov 2008: South Africa 0 Nigeria 1 (WAfcon)

4 Nov 2010: South Africa I Nigeria 2 (WAfcon)

3 June 2012: South Africa 1 Nigeria 1 (Friendly)

23 June 2012: Nigeria 0 South Africa 0 (Friendly)

7 Nov 2012: South Africa 1 Nigeria 0 (WAfcon)

22 Oct 2014: South Africa 1 Nigeria 2 (WAfcon)

29 Nov 2016: Nigeria 1 South Africa 0 (WAfcon)

18 Nov 2018: South Africa 1 Nigeria 0 (WAfcon)

1 Dec 2018: Nigeria 0 South Africa 0 (WAfcon) – Nigeria ta yi nasar 4-3 a bugun fenariti

21 Sept 2021: Nigeria 2 South Africa 4 (Aisha Buhari Cup)

4 July 2022: South Africa 2 Nigeria 1 (WAfcon)

5 April 2024: Nigeria 1 South Africa 0 (Oq)

Leave a comment