Ko Barca za ta ci Valencia ta koma ta biyu a teburin La Liga

Barcelona za ta kara da Valencia ranar Litinin a La Liga, karawar da idan ta yi nasara za ta koma ta biyun teburi.

Tun farko sun tashi 1-1 ranar 16 ga watan Disambar 2024 a karawar bana, inda Barca ta fara cin kwallo ta hannun Joao Felix, bayan da suka koma zagaye na biyu daga baya Valencia ta farke ta hannun Hugo Guillamon.

Real Madrid ce ta daya da maki 84, sai Girona ta biyu mai maki 71 da kuma Barcelona ta uku da maki 70.

Ita kuwa Valencia wadda take ta takwas a teburin La Liga mai fatan samun gurbin shiga gasar zakarun Turai a badi tana da maki 47 kawo yanzu.

Bayan da Barcelona ta yi rashin nasara a karawar El Clasico ta kwan da sanin tana bukatar cin wasannin dake gabanta, bayan da Real ta bata tazarar maki 14.

Yanzu dai fatan Barcelona mai La Liga na bara na fatan zama ta biyu a teburin kakar bana, hakan zai ba ta damar samun gurbin Champions League kai tsaye na badi da kuma shiga gasar Spanish Super Cup.

Barcelona na fuskantar kalubale daga abokiyar hamayya Girona a gurbin shiga Spanish Cup na badi, wadda ta doke Las Palmaers 2-0 a La Liga ranar Asabar.

https://twitter.com/FCBarcelona/status/1784840274033664247

Kenan idan Barcelona ta yi nasara a kan Valencia ranar Litinin za ta koma ta biyu da tazarar maki biyu tsakaninta maki biyu tsakani da Girona.

Leave a comment